IQNA

Babban Gangamin Al'ummar Iraki Domin Goyon Bayan Al'ummar Falastinu

23:58 - May 15, 2021
Lambar Labari: 3485919
Tehran (IQNA) al'ummar kasar Iraki sun gudanar da babban gangami a yau Asabar domin nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu.

A daidai lokacin da kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai a yankin zirin Gaza suke ci gaba da harba makaman roka a kan birnin Tel Aviv babban birnin Haramtacciyar kasar Isar’ila, shugaban jam’iyyarsa siysa ta Sadr a kasar Iraki sayyeed Muqtadha Assadr ya bukaci Irakawa su fito zangar zangar yin allawadai da ta’asar da haramtacciyar kasar Isara’ila take tafkawa a Falasdinu da suka mamaye.

Sadr ya bukaci a kiyaye ka’idojin kiwon lafiya saboda hana yaduwar cutar korona a gangamin na yau Asabar, sannan ya ce dole ne a daga tukar  Falasdinu, sannan a kona tutocin Isra’ila da Amurka mai goyon bayanta.

A wani rahoton kuma Khalid Mash’al shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas a wajen Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa dole ne a kiyaye sharuddun tsagaita bude wuta tsakanin Hamas da sojojin Isra’ila a duk wata tsagaita bude wuta da za’a yi nan gaba.

Haka nan ya kuma kara da cewa dole ne a dakatar da korar falasdinawa a yankin sheikh Jarrah wanda hakan ne ya haddasa rikici na baya-bayan nan.

Sannan a cire duk shingaye masu hana Falasdinawa isa masallacin Al-Aqsa da kuma sakin duk Falasdinawan da aka kama a baya-bayan nan.

 

3971574

 

captcha