IQNA

An Kammala Aikin Saka Sabon Kyallen Dakin Ka'abah Mai Alfarma

21:48 - July 19, 2021
Lambar Labari: 3486119
Tehran (IQNA) a yau an kammala aikin saka sabon kyallen dakin Ka'abah mai alfarma bayan kammala aikin wanke dakin Ka'abah.

A kowace shekara a daidai rana irin ta yau 9 ga watan Zulhijja wanda shi ne ranar tsayuwar Arafat, ake kammala aiki saka sabon kyallen dakin Ka'abah, bayan wanke shi da ruwan wardi.

Fadin kyallen dai ya kai mita murabba'i 658, sannan kuma tsawonsa ya kai mita 14, sannan kuma aikin dinka wannan kyalle ya kan dauki akalla watanni 8 ana gudanar da shi.

Ana gudanar da wanann aiki ne a wani wuri da ke cikin bangaren haramin Makka, inda masu aikin sukan yi amfani da bakin alhariri wajen sake kyallen.

baya ga haka kuma ana yin sakar ne tare da yin afmani da fasahar rubutu da zaren sakar a kan wannan kyalle, kamar yadda kuma ana yin amfani da zare mai ruwan zinari wajen ruburun ayoyi da sunayen Allah da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.

 

3984678

 

Abubuwan Da Ya Shafa: haramin makka
captcha