IQNA

Sakon Shugaba Rauhani Na Taya Shugabannin Kasashen Musulmi Murnar Idin Layya

22:03 - July 21, 2021
Lambar Labari: 3486126
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya isar da sakon taya murnar idin sallar layya ga shugabannin kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon nasa wanda ya aike wa shugabanni daban-daban na kasashen musulmi, shugaba Rauhani ya bayyana wannan lokaci na idin sallar layya da cewa, lokaci mai matukar muhimmanci ga dukkanin al’ummar musulmi.

Ya ce lokaci na gudanar da ibadar aikin hajji, wadda take daya daga cikin manyan rukunai na addinin muslunci, ibadar da ke hada dukkanin musulmi daga ko’ina cikin fadin duniya domin tabbatar da Kalmar tauhidi da yin aiki da umarnin Allah.

Shugaba Rauhani ya bayyana cewa, har kullum musulmi suna da bukatuwa zuwa ga karfafa alakarsu da kuma kaunar juna, da yin aiki tare a dukkanin bangarori domin ci gabansu, da kuma fuskantar kalu bale da ke a gabansu a mataki na duniya.

 

3985503

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karfafa alaka fadin duniya rukunai
captcha