IQNA

Duniya Na Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Harin Daesh A Birnin Bagadaza

22:35 - July 21, 2021
Lambar Labari: 3486127
Tehran (IQNa) Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya dagane da harin ta’addancin da aka kai a kasar Iraki.

A cikin wani bayani da ya fitar a jiya, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, harin da aka kai a unguwar Sadr da ke cikin birnin Bagadaza na kasar Iraki abin ban takaici ne kuma abin Allawadai.

Ya ce majalisar dinkin duniya tana bayar da cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar Iraki da kuma sauran al’ummar kasar, wajen tunkarar ayyukan ta’addanci da ke neman sake dawowa a kasar, tare da taya iyalan dukkanin wadanda suka rasa rayukansu alhinin abin da ya faru.

A nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta bayyana harin a matsayin aiki na dabbanaci, wanda ya yi hannun riga da ‘yan adamtaka, tare da yin kira da a tabbatar da an kame dukkanin masu hannu a cikin lamarin, domin su fuskanci sakamakon aikinsu.

Kasashen duniya da dama da suka hada da Iran, Aljeriya, Rasha, kungiyar kasashen larabawa da kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa, duk sun yi Allawadai da harin.

A ranar Litinin da ta gabata ce dai aka tayar da bama-bamai a cikin wata kasuwa da ke cikin unguwar sadr da ke gabashin birnin Bagadaza na kasar Iraki, a lokacin da mutane suke hadahadar sayayyar salla, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16, tare da jikkatar wasu da dama, da kuma jawo asara ta dukiyoyi masu yawa.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh dai ita ce ta dauki alhakin kai wannan hari, wanda yake zuwa a daidai lokacin da al’ummar kasar suke kira zuwa ga ficewar sojojin mamaya na Amurka daga kasar.

3985514

 

 

 

 

captcha