IQNA

Saudiyya: An Samu Nasarar Aiwatar Da Tsarin Kiwon Lafiya A Hajjin Bana

23:03 - July 22, 2021
Lambar Labari: 3486130
Tehran (IQNA) hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da cewa, an samu nasara wajen aiwatar tsarin kiwon lafiya a aikin hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, hukumomin kasar sun sanar da cewa, an samu nasara wajen aiwatar tsarin kiwon lafiya a aikin hajjin bana.

Ministan kiwon lafiya na kasar Saudiyya Taufiq Rabi'a ya bayyana cewa, an samu gagarumar nasara a tsarin kiwon lafiya da suka yi aiki da shi a hajjin bana, musammana  bangaren dakile yaduwar cutar corona a yayin aikin hajji.

Ya ce tun da aka fara gudanar da aikin hajjin ya zuwa yau babu wani daga cikin mahajjata da ya kamu da cutar corona, kamar yadda kuma dama dukkanin mhajjatan ba su dauke da cutar.

Ministan ya ce dukkanin matsalolin da aka samu na rashin lafiya ba su da alaka da corona, kuma babban abin da ya kara taimawa shi ne yadda mutane suka kiyaye ka'idojin da aka shata.

 

3985771

 

 

captcha