IQNA

Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Bukaci Ficewar sojojin Amurka Baki Daya Daga Kasar

22:30 - August 03, 2021
Lambar Labari: 3486167
Tehran (IQNA) 'yan gwagwarmaya masu yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a Iraki sun bukaci Amurka ta fitar da sojojinta daga kasar baki daya.

Kungiyar gwagwarmaya ta Nujba a kasar Iraki ta yi gargadin cewa, ba za ta amince da wanzuwar kowane nau’I na sojojin Amurka a cikin kasar Iraki ba.

A lokacin da yake zantawa da ta tashar talabijin ta Alalam a daren jiya, Nasr Alshummari kakakin kungiyar Nujba, wadda babban bangare ce na dakarun sa kai na al’ummar Iraki na Hash Alshaabi, ya bayyana cewa suna nan daram a kan bakansu na neman Amurka ta fitar da dukkanin sojojinta daga cikin kasar Iraki baki daya.

Alshummari ya ce, babu wani alhairi tattare da kasantuwar sojojin Amurka a cikin kasar Iraki, maimakon hakan ma sai matsaloli da suke haddasa wa kasar, baya ga cutar da ita da suke yi ta fuskoki daban-daban.

Ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin shugaban Amurka Joe Biden da kuma Firayi ministan Iraki da ba yawun al’ummar kasar Iraki aka shirya ta ba, domin kuwa al’ummar Iraki na bukatar ficewar sojojin Amurka ne baki daya, ba wani bangare daga cikinsu ba.

A yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin biden da Alkazimi, sojojin Amurka masu yaki za su fice daga Iraki daga nan zuwa karshen wanann shekara, yayin da sojoji masu bayar da shawara da horo ga sojojin Iraki za su ci gaba da kasancewa  a cikin kasar.

Tun bayan kisan da Amurka ta yi mataimakin babban kwamandan rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Abu mahdi almuhandis tare da Qasem Sulaimani a farkon shekarar 2020, majalisar dokokin Iraki bisa matsin lambar al’ummar kasar, ta kada kuri’ar amincewa da kudirin da ke neman Amurka ta fitar da dukkanin sojojinta daga cikin kasar Iraki.

 

3987954

 

captcha