IQNA

Malamin Da Musuluntar Da Mutane Fiye Da Dubu 100 A Kasashen Duniya Ya Rasu

23:00 - August 04, 2021
Lambar Labari: 3486171
Tehran (IQNA) Ni'imatullah Khalil Ibrahim Yurt malami ne dan kasar Turkiya wanda ya musuluntar da mutane fiye da dubu 100 a duniya.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, Ni'imatullah Khalil Ibrahim Yurt malami dan kasar Turkiya wanda ya musuluntar da mutane fiye da dubu 100 a duniya, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.

Ya rasu nea  wani asibiti da ke birnin Istanbul a jiya Talata, kuma an gudanar da janazarsa yau Laraba a garin Amasiyya.

An haifi Ni'imatullah Khalil Ibrahim Yurt a Lardin Amasiya da ke arewacin kasar Turkiya a shekara ta 1931, inda ya fara karatun addini tun daga lokacin rayuwarsa ta kuruciya.

A cikin shekara ta 1955 ya kasance babban ladanin babban masallacin birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, kuma mataimakin babban limamin masallacin.

Daga bisani ya koma kasar Saudiyya, inda ya rayua  can tsawon shekaru 33, inda ya rika koyarwa a masallacin Mahallat Asharf da ke yankin Jabal Nur a kasar Saudiyya.

Daga bisani musulmin kasar Japan sun roke shi da ya koma kasarsu domin koyar da sua ddinin muslunci, a lokacin ne ya karba kiransu ya koma kasar Japan da zama, inda ya kwashe tsawon shekaru 20 a kasar, ya gina daruruwan masallatai da makarantun addinin muslunci a kasar Japan.

Ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da dama domin yin wa'azi da yi wa mutane wadanda ba musulmi bayani kan addinin muslunci.

Adadin mutanen da ya musluntar a rayuwarsa sun haura dubu 100, musamamna  kasar Japan, inda yafi gudanar da ayyukansa na yada addinin musulunci.

 

captcha