IQNA

Iraki: Jami'an Tsaro Sun Shirya Domin Gudanar Da Ayyukan Tsaro A Lokacin Ziyarar Arba'in

16:34 - September 15, 2021
Lambar Labari: 3486312
Tehran (IQNA) jami'an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba'in.

Kamfanin dillancin labaran alfurat News ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Usman alghanimi ya bayyana cewa, a halin yanzu jami'an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba'in nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami'an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.

Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la'akari da matsalolin da aka rika samu a  lokutan baya na hare-haren 'yan ta'adda lokacin tarukan addini a kasar.

Yanzu haka dai jama'a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba'in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki.

 

3997698

 

 

captcha