IQNA

Jami'an Leken Asirin Iran Sun Tarwatsa Gungun Wasu 'Yan Ta'adda A Cikin Kasar

16:55 - September 16, 2021
Lambar Labari: 3486315
Tehran (IQNA) Jami’an leken asiri na kasar Iran sun sanar da gano gungun wasu ‘yan ta’adda a cikin kasar, kuma tuni aka tarwatsa su.

A cikin wani bayani da ma’aikatar kula da tattara bayanan sirri ta kasar Iran ta fitar, ta sanar da cewa jami’anta na farin kaya sun gano wasu gungun ‘yan ta’adda a cikin kasar, wadanda suke aiwatar da wasu ayyukan ta’addanci a kan wasu muhimman wurare na kasar.

Bayanin ya ce an gano mutanen baki dayansu a wani aiki mai sarkakiya da jami’an taso na farin kaya suka kaddamar, wanda kuma ba a yi bayanin makomar mtunane ba, amma dai an bayyana cewa suna da alaka ne kai tsaye da wasu kasashe masu adawa da kasar ta Iran.

A lokuta da dama jami’an leken asirin kasar Iran sun sha sanar da kame irin wadannan mutane a yankuna daban-daban na kasar, wadanda sukan kai hari a kan muhimman wurare a cikin kasar, wadanda su kan bayyana bangarorin da ke daukar nauyinsu wajen yin hakan, daga ciki kuwa har wasu kasashen turai da na larabawa da kuma Isra’ila.

 

3997855

 

captcha