IQNA

Wasu Kasashen Musulmi Sun Taimaka Wajen Gina Masallatai A Kasar Uganda

21:30 - September 17, 2021
Lambar Labari: 3486319
Tehran (IQNA) wasu daga cikin kasashen musulmi sun taimaka wajen sake gyarawa ko gina masallatai a Uganda

Shafin yenisafak.com ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin kasashen musulmi sun taimaka wajen sake gyarawa ko gina masallatai a Uganda.

Kasashen da suke taimakawa wajen gudanar da irin wadannan ayyuka akwai wasu daga cikin kasashen larabawan yankin Tekun fasha, da kuma wata kungiyar jin kai ta kasar Turkiya.

Mafi yawan masallatan da ake gyarawa dai a kasar ta Uganda suna yankuna ne karkara, wadanda mazauna cikinsu ba su da galihu sosai balantana su iya samun damar gyaran masallatan nasu.

Daya daga cikin abin da aka san musulmin kasar Uganda da shi, shi ne zaman lafiya da kyakkyawar fahimtar juna tsakaninsu da sauran mabiya addinai na kasar, duk kuwa da cewa su ne marasa rinjaye idan aka kwatanta su da kiristoci a kasar.

A kasar Uganda akwai musulmi miliyan 12 daga cikin mutane miliyan 45 da ke kasar wadda take a gabashin nahiyar Afirka.

 

 

3997586

 

 

captcha