IQNA

An Bude Cibiyar Koyar Da Ilmin Kur'ani A Birnin nablus Na Falastinu

22:58 - September 21, 2021
Lambar Labari: 3486337
Tehran (IQNA) an bude cibiyar koyar da ilmomin kur'ani mai tsarkia birnin Nablus an Falastinu

Shafin yada labarai na Dunya Watan ya bayar da rahoton cewa, a yau an bude cibiyar koyar da ilmomin kur'ani mai tsarkia birnin Nablus an Falastinu, da nufin horar da yara da matasa kan ilmomin kur'ani mai tsarki.

Abu Rab wakilin ma'aikatar kula da harkokin addini ta Falastinu shi ne ya jagoran bude wannan cibiya, tare da halartar malamai da kuma jami'ai gami da al'ummar gari.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron kaddamar da wannan cibiya, Abu Rab ya bayyana cewa, wannan cibiya za ta mayar da hankali wajen samar da matasa Falastinawa masu gogewa kan lamarin kur'ani.

Baya ga koyar da karatu da hukunce-hukuncensa, cibiyar za ta mayar da hankali wajen samar da matasa mahardata kur'ani mai tsarki.

Sannan kuma baya ga ilmomin da suka shafi kur'ani, za a rika koyar da wasu ilmomin na addini domin sanin sauran bangarori na addinin muslunci.

 

3998972

 

captcha