IQNA

Majami'ar Katolika A Canada Ta Nemi Afuwa Kan Kisan 'Yan Asalin Kasar

23:02 - September 25, 2021
Lambar Labari: 3486350
Tehran (IQNA) majami'ar Katolika a kasar Canada ta nemi afuwa kan kiyashin da aka yi wa 'yan asalin kasar.

Kamfanin dillancin labaran France 24 ya bayar da rahoton cewa, majami'ar Katolika a kasar Canada ta nemi afuwa kan kiyashin da aka yi wa 'yan asalin kasar.

Majami'oin mazhabar Katolika ta kiristoci sun nemi amfawa bisa abin da jami’an cocin suka aikata na kisan kiyashin yara ‘yan asalin kasar Canada a makarantun kwana wadanda suke karkashin kulansu kimani shekaru 100 da suka gabata.
 
Wannan na zuwa ne bayan gano kaburburan gama gari har guda 3 na yara ‘yan asalin kasar Canada wadanda aka gano a wasu jihohin kasar ta Canada a cikin wannan shekarar, wanda yawansu ya kai 1,200 ya zuwa yanzu. Kuma har yanzun ana ci gaba da amfani da wasu na’urorin Rada don gano karin irin wadannan kaburbura.
 
Bayan mamayar da turawan suka yiwa kasar Canada a karnuka da suka gabat malaman mazahbar katolika sun bude makarantu na kwana, inda suke kula da ‘ya’yan kabilun da suka samu a kasar, amma kuma a boye suka kashe da dama daga cikinsu.
 
Shuwagabannin kabilun asalin kasar Canada sun ce za su amince da wannan afwa, amma suna son wata dawaga daga kasar ta je kasar Italiya don ganawa da paparoma kan batun kafin ya kawo ziyarar ganin ido kasar.
 

3999932

 

 

captcha