IQNA

Alaka Na Ci Gaba Da Kara Habbaka Tsakanin Gwamnatin Sudan Da Yahudawan Isra'ila

16:48 - October 14, 2021
Lambar Labari: 3486424
Tehran (IQNA) Ministan shari’ar na Sudan ya gana da Ministan Ma’aikatar Hadin Kan Yankuna na Isra’ila a birnin Abu Dhabi.

Ministan shari’ar Sudan Nasruddin Abdul Bari da ministan na Isra’ila Issawi Furaij sun gana a jiya Laraba a birnin Abu Dhabi, babban birnin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ministocin biyu sun tattauna hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin kasar Sudan da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila a bangarori daban-daban, musamman a ayyukan ilimi da al'adu tsakaninsu.

Kafin wannan lokaci dai Sudan ba ta sanar da wannan ganawa ba, da kuma abubuwan da za ta za ta kunsa, amma dai hakan duk yana daga cikin matakan da sabuwar gwamnatin ta Sudan take dauka ne na karfafa lakar da ta kulla da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Yawancin ministocin gwamnatin yahudawan sahayoniya a halin yanzu suna cikin Hadaddiyar Daular Larabawa, domin halartar wani gagarumin biki na tunawa da ranar da kasashen larabawan suka sanya hannu kan kulla alaka da gwamnatin yahudawan, tare da wakilai daga kasashen Gabas ta Tsakiya guda shida, da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Bahrain, Sudan da Morocco, da kuma wakilan gwamnatin yahudawan sahyoniyawa.

Kwanaki kadan da suka gabata, tawagar sojojin Sudan karkashin jagorancin Mohammad Hamdan Daqlou, wanda aka fi sani da Hamidati, mataimakin shugaban majalisar gudanarwar ta Sudan, ya ziyarci amma ba a bayyana dalilan wannan tafiya ba.

Majiyoyin diflomasiyyar Sudan sun bayyana cewa Sudan na shirin sanya hannu kan yarjejeniyar daidaita alakar da ke tsakaninta da gwamnatin yahudawan Isra’ila a cikin wannan wata na Oktoba.

A watan Satumban shekara ta 2020, jami’an Isra’ila, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain suka sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu a Fadar White House da ke birnin Washington a kasar Amurka, wadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta.

Bayan wata daya, Isra’ila da Sudan sun sanar da aniyarsu ta kulla alaka, yayin da Morocco ta kulla huldar diflomasiyya da Isra’ila a watan Disamba na bara.

 

 

4004774

 

captcha