IQNA

Sallar Jam'i Ta Farko A Masallacin Haramin Makka Da Masallacin Ma'aiki (SAW) Bayan janye Dokar Corona

17:10 - October 17, 2021
Lambar Labari: 3486436
Tehran (IQNA) an gudanar da sallar jam'i ta farko a masallacin Haramin Makkah mai alfarma da kuma masallacin amnzon Allah (SAW) a Madina bayan janye dokar Corona.

Tashar Alarabiya ta bayar da rahoton cewa, bayan janye dokar Corona an gudanar da sallar jam'i ta farko a masallacin Haramin Makkah mai alfarma da kuma masallacin amnzon Allah (SAW) a Madina.

Bidiyoyin da aka watsa a kafafen yada labaran kasashen Larabawa sun nuna cewa a karon farko tun bayan barkewar cutar corona, limaman Masallacin Annabi (SAW) da Masallacin Harami suna neman masu ibada da su tsara layukan sallah.

Rage tsananta dokar gami da soke bayar da tazara a tsakanin jama’a da sanya abin rufe fuska a wuraren taruwar jama'a a Saudi Arabia, zai fara aiki daga yau.

A cikin wannan bidiyo zaku ga sallar jam’i ta farko a Masallaci Mai alfarma ba tare da tazara tsakanin jama’a ba.

 

4005727

 

Abubuwan Da Ya Shafa: madina
captcha