Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin karni na 19, kusan masu bauta 4000 ne a Aljeriya da ke zanga -zangar mayar da Masallacin Katshawe zuwa coci, sojojin mulkin mallaka na Faransa suka kashe a babban birnin kasar ta Aljeriya.
An gina masallacin ne a lokacin Daular Usmaniyya, Masallacin Katshawe da ke Aljeriya ba kawai daya ne daga cikin muhimman alamomin kasar ba, har ma da muhimmin abubuwa da ke a matsayin shaida kan laifukan gwamnatin mulkin mallaka ta Faransa a Aljeriya.
A wata hira da manema labarai na cikin gida, shugaban Aljeriya Abdel Majid Tebon ya gabatar da rahoton hukuma kan kisan kiyashin da aka yi wa masallata kusan dubu hudu a lokacin mulkin mallaka 1830-1962.