IQNA

Taliban Ta Damke Wali Na Daesh A Lardin Nangarhar

21:21 - October 18, 2021
Lambar Labari: 3486442
Tehran (IQNA) Taliban ta sanar da kame Wali na kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh a Lardin Nangarhar

Kamfanin dillancin labaran Sky News ya bayar da rahoton cewa, a yau Litinin Taliban ta sanar da kame Wali na kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh a Lardin Nangarhar da ke gabashin kasar Afghanistan.

Daruruwan 'yan kungiyar ta Daesh ko ISIS sun samu mafaka a lardin Nangarhar. Lardin ya kasance wani yanki na al-Qaeda, kuma an kafa al-Qaeda a cikin tsaunukan Tora Bora da ke a lardin.
 
A ranar 4 ga watan Oktoba, gwamnatin Taliban ta sanar da wani samame a kan kungiyar ISIS a Khorasan a gunduma ta 17 a Kabul.
 
Gwamnatin Taliban ta rubuta a shafinta na Twitter cewa samamen ya yi nasara sosai, kuma ya kai ga ragargaza  gungun 'yan ta'addan tare da kashe su baki daya.
 
Wannan farmakin ya biyo bayan sanarwar da kungiyar ISIL ta bayar ne, inda ta dauki alhakin hare -haren bama -bamai guda biyu da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a wajen filin jirgin saman Kabul, wanda ya kashe mutane 72, ciki har da sojojin Amurka 13, da kuma hare-hare kan masallatan Juma'a a cikin 'yan kwanakin nan.

 

4005981

 

 

 

captcha