IQNA

Nasrullah: Dole Ne Musulmi Su Hada Kansu Domin Tunkarar Kalubalen Da Ke A Gabansu

16:50 - October 20, 2021
Lambar Labari: 3486450
Tehran (IQNA) babban sakataren Hizbullah ya bayyana hadin kai a tsakanin musulmi a matsayin abin yake wajibi a kansu.

Babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar Labanon sayyid Hassan Nasrullah da yake bayani a gaban taron makon hadin kai karona 35 da ke gudana a birnin Tehran ya fadi cewa babban manufar gudanar da taron makon hadin kai shi ne samar da mafita game da kalubalen da duniya musulmi ke fuskanta
Ya ce duniya musulmi na fuskantar kalu bale sosai tun da kasashen duniya ma’abota girmankai da kasar Amurka ke jagoranta suka taso musulmi a gaba, duk da kokarin da aka yi na kusanto da alummar musulmi bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran.
 
Kana ya bukaci da a kafa kwamiti a gefen taron makon hadin kai yadda malamai da masana za su yi musayar ra’ayi da kuma samar da mafita ga duniyar musulmi kan halin tsaka mai wuya da suke ciki
 
Kimanin malam musulunci sama da 500 ne suke halartaci taron makon hadin kai tsakanin musulmi karo na 35 daga nesa saboda yaduwar Annobar Korona a fadin duniya, kuma babban abin da taron yafi mayar da hankali shi ne hadin kan musulmi da zaman lafiya da kuma nisantar rarrab da rikici a duniyar musulmi.
 

 

4006482

 

captcha