IQNA

Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Harin Ta’addanci A Syria Ya Karu Zuwa Ashirin Da Bakwai

18:35 - October 20, 2021
Lambar Labari: 3486451
Tehran (IQNA) adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin ta’addancin da aka kai yau Damascus ya karu zuwa ashirin da bakwai.

Rahotanni daga kasar Syria na cewa, adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin ta’addancin da aka kai yau Damascus ya karu zuwa 27.

An tayar da bama -bamai guda biyu a kan motar sojoji a tsakiyar birnin Damascus da sanyin safiya, inda suka kashe mutane 14 a matsayin hari mafi muni da aka kai babban birnin kasar cikin shekaru hudu.

Ya zuwa yanzu babu wani bangare da ya dauki alhakin  kai harin, sai dai kuma bayan wani dan lokaci da kai harin,  sojojin gwamnatin sun yi luguden wuta akan wasu sansanonin ‘yan ta’adda da gwamnatin Turkiya ke marawa baya a cikin Lardin Idlib da ke kan iyakokin kasashen biyu, wadanda suke da hannu wajen kai wasu hare-haren ta’addancin makamantan wannan a baya.

Kafofin yada labaran Syria sun ce, Kamfanin an kai harin ta'addanci ne ta hanyar tayar da wasu bama -bamai guda biyu a lokacin  wata motar bas da ke dauke da sojoji  take wucewa a wata babbar gada a cikin birnin Damascus, a kusa da gidan adana kayan tarihi na kasa da ke tsakiyar babban birnin na Syria.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa, adadin wadanda suka rasa rayukan nasu ya karu zuwa ashirin da bakwai daga bisani.

4006650

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha