IQNA

Rubutacciyar Makala Kan Ilimi Da Amfaninsa

19:32 - October 22, 2021
Lambar Labari: 3486459
Tehran (iqna) rubutacciyar makala kan ilimi da amfaninsa wadda jaridar Leadership Hausa ta buga.
Ilimi kowanne iri ne ya na da amfani, matukar ba hauka da shirme ba ne. ta hanya daya a ke gane ilmi da abin da ba ilmi ba, duk wani abu wanda ba zai taimakawa rayuwar al’umma ba ko kuma ba zai taimakawa ci gaba da kawo sauyi a yanayin da a ke ciki ba, wannan ba ilmi ba ne. watakila wani sunan ya ke da shi na daban.
 
Amfanin ilmi shi ne ya cire wa wanda ya same shi kangin duhun kai da kauyanci. Duk ilmin da ba zai wayar da tunanin dan Adam ba, wannan ba ilmi ba ne, ko kuma ba a shigar da ilmin yadda ya dace ba.
 
Wani abin dariya ga mutane shi ne sun yi zaton wai sai da Bature (me jan kunne) ya zo Nijeriya sannan a ka samu tumbatsar ilimi. Alhali zancen ba haka ba ne, tuntuni akwai ilimi a kasar hausa. Akwai maluman tarbiyya da akida a zaurukan kakanninmu, wadanda ke shigar da ilimin gina ruhi da kyakkyawar alaka a tsakanin al’umma.
 
Ko a yanzu idan ka samu wanda ya samo iliminshi daga irin wadancan zauruka, matukar bai canza alkibla ba, za ka ga cewa ya na da nutsuwa, sannan kuma gogagge ne a fannin da ya samu horo.
 
A baya, makarantu wuraren gina tarbiyya ne kawai, amma saboda sauye – sauye da a ke samu a cikin al’umma, sai ya kasance yanzu makarantu wuraren gina ginshikan da za su tallafawa ci gaban al’umma ne, hade da saita tarbiyya a lokaci guda.
 
Tun daga makarantar Firamare, akwai wani abu da a ke so a shigar a kwakwalen yara, ba wai kawai darussan su ABCD ko 1234 ba. a na kokarin a nuna musu muhimmancin kiyaye lafiya, son kasa, da kuma al’adunmu.
 
Kacokaf manufar ba ta takaita ga iya magana da turanci ko rubutu ba turanci ba, wadannan riba ne da a ke samu daga ilimi, amma ba wai shi ne makasudin yin ilimin ba. saboda idan da iya turanci da rubutu da shi ne, da sai na bayar da misalin Farfesan da ya kure gudun turanci amma kuma bai iya mu’amala da mutane ba, bai iya magana me dadi ba, bai iya tausasa lafazi ga manya da yara ba. uwa uba dabi’unsa ko Kare ba zai ci ba. Misalin wancan Farfesa shi ne na wanda ya ilmantu da tsuran ilmi, amma ba mai amfani ba.
 
Ilimi me amfani shi ne wanda mutum zai yi aiki da shi, ilimin da mutanen da ke kewaye da kai za su ci moriyarshi a rayuwarsu ta yau da kullum. Ba kawai tsabar kwarewa da fekewa ba, a’a, ya kasance ka na iya sarrafa wannan ilimi na ka domin tallafawa mutane.
 
A kasashen da su ka ci gaba, masu iliminsu ba wai kawai ‘yan kasar ke cin moriyarsu ba, kusan duk duniya a na amfana da su, saboda ba su dankwafe tunanin wuri daya ba, sannan akwai zuciyar samar da mafita ga rayuwar dan Adam.
 
Babban kalubalen da ke fuskantar kasashe masu tasowa shi ne, saboda tsananin rayuwa da a ke fama da ita. Yawancin mutane na zuwa makarantu ne su dage su yi ta bubbugawa kawai don su kai lokacin da za su rika samun na abinci. Wannan tunanin yin karatu saboda samun na abinci na daga cikin dalilan da su ka sa mutanenmu ba su tsayawa su sadaukar da iliminsu wurin taimakawa ci gaban al’umma da ma kasa baki daya.
 
Babban misali anan ita ce kasarmu ta Nijeriya, kusan duk wanda ya samu ilimi wadatacce, burnish shi ne ya samu damar da zai tsallake ya bar kasar domin ya tsira da rayuwarshi kamar yadda ya tsara tafiyar da ita. Saboda hukumominmu ba su da wasu shirye – shirye na gina rayuwar masu ilimi, wannan sai dai rayuwar ‘yan siyasa da ‘yan barandansu.
 
Akwai likitoci masu yawan gaske a Turai wadanda ke aikinsu a can, saboda abin sadakan da su ke samu a can ko kusa ba za a biya su a nan ba. haka kuma yadda a ke kare martabarsu da mutunta su, ko kadan hukumominmu ba su aikatawa wadanda ke nan. Hakkokin na su ma a wasu lokutan, sai sun hada da yajin aiki sannan a ke samu a gutsura musu.
 
Irin wannan hali da mu ke ciki ne, ke ba masu ilimi tsoron ci gaba da zama a tare da mu. Wadanda idan da za su kasance a nan, da ci gaban da za mu samu sai ta ninninka matsayar da mu ke a wannan bigire.
 
Akwai injinoyin kwamfuta da na mota, akwai masana kere – kere da sauransu. Haka nan akwai masana halayyar jama’a da zamantakewar al’umma rututu a wasu kasashen, inda su ke can su na taimakawa wadancan al’ummu wurin saita tunani da rayuwarsu tare da samar da hanyoyin zaman lafiya da magance duk wata barazana ga ci gaban al’umman.
 
Mu kuma mu na nan sai kashe kawunanmu mu ke yi, sai muguwar keta da hassada, sai mugayen dabi’u da sharrace – sharrace a tsakani, wadanda su ne sanadin dankwafewar mu.
 
Ya kamata masu ilimin da su ka rage a cikin gida, wadanda su ka jurewa wahalhalun da su ke sha a Nijeriya, su tashi haikan su kammala aikinsu na tabbatar da iliminsu a aikace a cikin wannan al’umma ta mu.
 
Saboda fata na gari na a hannun masu ilimi, su kuwa masu ilimin ba shashashu ba, a’a wadanda ke amfani da shi, wadanda ilimin ya yi tasiri a kan dabi’unsu, idan sun yi magana a ji ilimi, idan sun aikata aiki a ga ilimi, wannan shi ne amfanin ilimi. 
 
Daga: Leadership Hausa
captcha