IQNA

Ana Shirin Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Cibiyar Azhar A Kasar Masar

23:23 - October 23, 2021
Lambar Labari: 3486466
Tehran (IQNA) Cibiyar Azhar ta yi bayani kan gudanar da gasar kur'ani mai tsarki shekara ta uku a jere.

Al-Azhar na gudanar da gasar Alkur'ani Mai Girma ta shekara-shekara, a shekarar ilimi ta 2021-2022 karkashin jagorancin Sheikh Ahmad Al-Tayyib, shugaban cibiyar.

Babban daraktan kula da harkokin kur’ani mai tsarki na sashin kwalejin Azhar ya bayyana cikakken bayani kan gasar da za a yi shekara ta uku a jere da sunan Ahmad Al-Tayyib Sheikh Al-Azhar.

Za a gudanar da gasar haddar kur'ani mai tsarki ta sheik Al-Azhar ne a matakai biyu, matakin farko za a gudanar da shi ne daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 26 ga watan Nuwamba, sannan za a sanar da ranar da za a kammala matakin karshe.

Matakin farko na gasar haddar kur’ani ta Sheikh Al-Azhar za a gudanar da shi ne a hedkwatar cibiyar Azhar da sassan ilimi ta hanyar kwamitoci na cikin gida da aka kafa a kowace gunduma, wadanda suka samu maki sama da 80 cikin 100 za su kai matakin karshe.

A mataki na biyu na gasar Azhar, za a bayar da kyautuka ga daliban da suka samu maki sama da 90.

 

4007240

 

captcha