IQNA

Babban Masallacin Al Jazeera Na Aljeriya Ya Lashe Kyautar Gini  Mafi Kyau Da Tsari Ta Duniya

14:33 - November 22, 2021
Lambar Labari: 3486590
Tehran (IQNA) Babban Masallacin Al Jazeera ya sami lambar yabo ta Amurka ta 2021 ta gini mafi kyau a daga Gidan Tarihi na Gine-gine na Chicago da Cibiyar Fasaha ta Turai.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Ofishin Jakadancin Amurka da ke kasar Aljeriya ya wallafa wani rubutu a shafinsa na yanar gizo, inda ya sanar da taya Aljeriya murnar zabar masallacin Algiers a matsayin daya daga cikin mafi kyawun ayyukan gine-gine na kasa da kasa a shekarar 2021.

Inda aka bayyana wannan masallacin da ke karbar bakuncin dubban daruwan mutane a matsayin wanda ya cancanci kyautar gine-gine mafi kyawu da tsari ta cibiyar Chicago.

Ofishin jakadancin ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar: Kamfanin gine-ginen Jürgen Engel, da suka kware kan harkokin gine-gine a Jamus ne ya yi zanen babban masallacin, wanda kuma dukkanin masana gine-gine na duniya sun yaba da tsarinsa.

A bana, an bayar da lambar yabon ta zabo gine-gine da ayyukan raya birane daga kasashe daban-daban da suka kai 35, da suka hada da Algeria, Austria, Australia, Azerbaijan, Brazil, Belgium, Canada, China, Denmark, Finland, Faransa, Girka, Jamus, Hong Kong, Indonesia, Italiya. Japan, Mexico. Netherlands, Norway, Portugal, Qatar, Rasha, Singapore, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, Spain, Switzerland, Taiwan, Thailand, Hadaddiyar Daular Larabawa, Burtaniya, Amurka, Uruguay da Vietnam.

 

4015112

 

captcha