IQNA

Taliban Da Amurka Za Su Koma Teburin Tattaunawa A Qatar

22:09 - November 24, 2021
Lambar Labari: 3486601
Tehran (IQNA) wakilan gwamnatin Taliban da na gwamnatin Amurka za su koma teburin tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa,a  yau Laraba ma'akatar harkokin waje ta gwamnatin Taliban ta sanar da cewa, wakilan gwamnatin Taliban da na gwamnatin Amurka za su koma teburin tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar.

A cewar ma'aikatar, wakilin Washington a Afghanistan zai koma Doha a mako mai zuwa don jagoran tawagar Amurka a tattaunawa da Taliban.
 
Sanarwar da Taliban ta fitar ta ce, za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Taliban da Amurka domin nazarin dangantakar siyasa da matsalolin tattalin arziki a Afghanistan, da kuma aiwatar da yarjejeniyar Doha wadda aka rattaba hannu kanta a baya.
 
Tun da farko ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da cewa za ta fara tuntubar kungiyar Taliban a mako mai zuwa, inda za ta tattauna muhimman batutuwan da suka shafi Afganistan, ciki har da yaki da ta'addanci.
 

 

 

captcha