Kamfanin dillancin labaran Safa ya bayar da rahoton cewa, dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta tilasta wa masu ibada shiga masallacin ta kofar tsohon birnin da kuma takura su.
Dakarun mamaya sun kafa shingaye a kofar shiga tsohon birnin da ke kan hanyar zuwa Masallacin Al-Aqsa, inda suka yi wa matasan tambayoyi tare da duba kowannen su, tare da duba kayansu da jakunkuna.
Masu ibada a masallacin Al-Aqsa sun gudanar da addu'o'i ga ruhin shahidai. An sanya manya-manyan tutoci a farfajiyar masallacin, a jikinsu akwai hotunan shahidai guda biyu Fadi Abu Shekhidam da Al-Fati Omar Abu Asb.
'Yan sandan gwamnatin mamaya sun kai farmaki a masallacin Al-Aqsa bayan sallar Juma'a tare da kwashe hotunan shahidan biyu.
Ofishin bayar da agajin gaggawa na Musulunci ya sanar da cewa, masallata 40,000 ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa a yau.
https://iqna.ir/fa/news/4016376