IQNA

Nasrullah: Saka Sunan Hizbullah A Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda ba Shi Da wani Tasiri A kan Kungiyar

2:51 - November 27, 2021
Lambar Labari: 3486610
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa, saka kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda ba shi da wani tasiri a kan kungiyar.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a yau babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar da jawabi wanda aka watsa kai tsaye a kafofin yada labarai na ciki da wajen Lebanon, dangane da halin da ake ciki a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya.

Da farko dai ya fara ne da taya al'ummar kasar muranar zagayowar ranar samun 'yancin kasar daga mulkin mallaka na turawan kasar Faransa a kan kasar Lebanon.

Ya ci gaba da cewa, duk da cewa kasar ta samu 'yanci a hukumance, to amma abin tambaya shi ne shin 'yancin da kasar ta samu da gaske ne ko kuwa rubutu ne kawai a kan takarda? domin kuwa abubuwa da dama da suke faruwa dangane da kasar na nuni da cewa har yanzu kasar ba ta zama mai cikakken 'yancinta ba.

Ya bayar da misali da mamayar da Isra'ila ta yi wa kasar Lebanona  shekarun baya, wanda wannan ne babban dalilin kafa kungiyar Hizbullah wadda ita ce ta fatattaki Isra'ila daga Lebanon, inda ya ce kungiyar Hizbullah za ta ci gaba da kasancewa a cikin shiri a kowane lokaci, matukar dai kasar Lebanon tana fuskantar barazana daga Isra'ila kamar yadda duniya take ji kuma take gani Isra'ila na yi.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya ce, saka kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda ba shi da wani tasiri a kan kungiyar da kuma ayyukanta, kamar yadda hakan ba zai iya rage karfinta ko sanyawa ta canja manufarta ta kare Lebanon daga barazanar yahudawan Isra'ila ba.

 

https://iqna.ir/fa/news/4016394

captcha