IQNA

Ana Gudanar da Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Kulla Hulda Da Isra'ila A Fadin Kasar Morocco

21:32 - November 28, 2021
Lambar Labari: 3486616
Tehran (IQNA) al'ummar kasar Morocco suna gudanar da zanga-zanga a dukkanin amnyan biranen kasar domin yin tir da Allawadai da kulla alaka da Isra'ila.
Kungiyar kare hakkin al'ummar Falasdinu mai zaman kanta a kasar Maroko a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce fiye da garuruwa 27 na kasar Morocco ne suka mayar da martani mai kyau dangane da ranar hadin kai da al'ummar Palasdinu da ake gudanarwa a ranar 29 ga watan Nuwamban kowace shekara. inda suka fara gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga al'ummar Falastinu.
 
Sanarwar ta kara da cewa: Za a gudanar da zanga-zangar kuma a gobe Litinin da kuma jerin gwano mai taken ci gaba da gwagwarmaya don dakile daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniya da kuma tallafawa al'ummar Palastinu.
 
 
A cewar sanarwar, wadannan tarukan zanga-zangar nuna goyon baya ga gwagwarmayar 'yantar da al'ummar Palastinu daga hannun yahudawan sahyuniya da kuma kafa kasar Palasdinawa dimokuradiyya a duk fadin yankunan Palasdinawa za su kasance ne a dukaknin biranen Moroco.
 
Sanarwar da kungiyar kare hakkin Falasdinu a kasar Maroko ta fitar ta bayyana cewa, manufar wannan mataki ita ce watsi da kulla alaka da gwamnatin sahyoniyawan mamaya da kuma neman soke dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin Moroko da wannan gwamnati.

 

 

4016784

 

captcha