IQNA

Jordan Ta Yi Allawadai Da Kalaman Isla'ila Dangane Da Masallacin Quds

21:08 - November 30, 2021
Lambar Labari: 3486625
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Jordan ta yi Allawadai da furucin gwamnatin Isra'ila na halasta gina wani wurin bautar yahudawa a cikin harabar masallacin Quds

Tahar TRT ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Jordan ta yi Allawadai da furucin gwamnatin Isra'ila na halasta gina wani wurin bautar yahudawa a cikin harabar masallacin Quds mai alfarma.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Jordan Haitham Abu al-Faul ya fitar, ya bayyana kalaman na Isra'ila a matsayin tsokana da rashin hujja kan masallacin Al-Aqsa.
 
Abu al-Ful ya kara da cewa: Wadannan maganganu an yi Allah wadai da su, kuma an yi watsi da su, kuma ana daukar su a matsayin babban cin zarafi na tarihin masallacin Al-Aqsa.
 
Abu al-Ful ya jaddada cewa gaba dayan masallacin Al-Aqsa da farfajiyarsa na mallaki ne na al'ummar musulmi.
 
Ya yi nuni da cewa: Ofishin da ke bayar da kulawa ga ayyukan masallacin da ke birnin Kudus, da kuma kuma hukumar harkokin masallacin Al-Aqsa ta kasar Jordan wadda ita ce hukumar da bangarorin kasa da kasa suka mika wa lamarin kula da Quds a bisa tsari na majalisar dinkin duniya, duk wannan na tabbatar da cewa larabawa da musulmi suke da hurumin kula da masallacin ba yahudawa ba.

 

4017542

 

captcha