IQNA

A Karon Farko Bangaladesh Ta Bai Wa 'Yan Rohingya Damar Ziyartar Danginsu

22:01 - December 01, 2021
Lambar Labari: 3486630
Tehran (IQNA) Dubban 'yan gudun hijirar Rohingya da aka aika zuwa tsibirin Basanchar na Bangladesh an ba su izinin ziyartar 'yan uwansu a karon farko.

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, a karon farko tun lokacin da suka yi ƙaura shekaru biyu da suka wuce, dubban 'yan gudun hijirar Rohingya da aka aika zuwa tsibirin Basanchar na Bangladesh an ba su izinin ziyartar 'yan uwansu.

Dubban daruruwan mutane suka tsere daga Myanmar a shekara ta 2017 bayan da sojoji suka murkushe su.
 
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar Bangladesh sun soki lamirin shirinta na tsugunar da ‘yan gudun hijirar Rohingya, da nufin mayar da ‘yan gudun hijira kimanin 100,000 zuwa tsibirin Basan Char domin rage cunkoso a birnin Cox’s Bazar da ke gabar teku.
 
Tsibirin na da saurin samun ambaliyar ruwa  da guguwa sakamakon sauyin  yanayi da ake samu, wanda hakan yana da matukar hadari ga 'yan gudun hijira.
 
Wani mai magana da yawun sojojin ruwan Bangladesh ya shaidawa kamfanin dillancin labaren AFP a yau Laraba cewa wani jirgin ruwa na kasar Bangladesh ya kai su Chittagong kuma daga can aka kwashe su da motocin bas guda biyu zuwa sansanonin.
 
Wannan shi ne karon farko da 'yan kabilar Rohingya da ke zaune a tsibirin ke zuwa sansanoni don ziyartar 'yan uwa.
 

4017752

 

captcha