IQNA

Isra'ila Ta Hana A Kammala Aikin Gyaran Masallacin Annabi Ibrahim (AS)

21:56 - December 08, 2021
Lambar Labari: 3486659
Tehran (IQNA) A jiya Talata sojojin gwamnatin Isra'ila sun hana ci gaba da gudanar da ayyukan kwamitin sake gina birnin Hebron wajen gyara masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke birnin Alkhalil a Falastinu.

Sheikh Hafizi Abu Sanineh, daraktan kwamitin hubbaren Ibrahimi ya bayyana cewa: A jiya ne dakarun gwamnatin sahyoniyawan suka hana kwamitin sake gina haramin na Al-Khalil ci gaba da aikin gyaran hubbaren Ibrahimi, wanda ya hada da gyaran layukan wutar lantarki da gyaran rufin masallacin, da kuma fentin bangayensa, gami da tsaftace masallacin mai tsohon tarihi.

Ya kara da cewa: “Aikin gyaran masallacin Annabi Ibrahim (AS) daya ne daga cikin ayyukan ma’aikatar wakafi da al’amuran addini da kuma hadin gwiwa da kwamitin sake gina birnin Alkhalil.

Kuma a cewarsa ana aiwatar da wadannan ayyukan ne a daidai lokacin yahudawan sahyuniya suke ta kara fadada mamayar yankunan birnin ta hanyar gina matsunnai.

Babbar manufar hakan dai ita ce raunana musulmin birnin, tare da shirin kwace masallacin Annabi Ibrahim daga hhannaun musulmi, domin mayar da shi wurin bautar yahudawa.

Ya ci gaba da cewa, wannan birni na musulmi zai ci gaba da kasancewa a hannun musulmi, tare da yin tsayin daka wajen kare shi da kuam kare masallacin annabi Ibrahim daga duk wani yunkurin keta akfarmarsa daga bangaren yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi.

 

4019400

 

 

 

captcha