IQNA

Putin Ya Ce: Cin Zarafin Manzon Musulunci (SAW) Ba ‘Yancin Fadar Albarkacin Baki Ba Ne

23:13 - December 23, 2021
Lambar Labari: 3486721
Tehran (IQNA) A wata ganawa da yayi da manema labarai, shugaban na Rasha ya bayyana cewa, cin zarafin Annabi Muhammadu (SAW) ba 'yancin fadar albarkacin ba ke ba ne.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a taron manema labarai da ya saba gabatarwa kafin ranar kirsimatia  kowace shekara, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya jaddada cewa, babu yadda za a yi keta alfarmar  wani abu mai tsarki a wajen wasu mutane ko abin da suke girmamawa, hakan ya zamanto cikin 'yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi.

Ya kara da cewa: Irin wadannan ayyuka na iya haifar da karin kiyayya da tsattsauran ra'ayi a duniya.
 
A wani bangare na taron manema labarai, Putin ya amsa tambayar ko Rasha za ta amince da kungiyar Taliban a hukumance, inda ya ce: samun daidaiton dangantaka da Afghanistan na daya daga cikin muhimman batutuwan tsaron kasa ga Rasha.
 
Ya kara da cewa: "Abu mafi muhimmanci da ya kamata a yi a halin yanzu a Afganistan shi ne hana rugujewar kasar; Kasashen da suka mamaye Afganistan tsawon shekaru 20 ya kamata su kasance a sahun gaba a kasashen da ke ba da taimako ga Afghanistan.
 
A kowace shekara, shugaban na Rasha yana bayyana ra'ayinsa kan batutuwa daban-daban a wani taron manema labarai, wanda aka saba gudanarwa kafin Kirsimeti.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4023053

 

captcha