IQNA

Hizbullah: Ya Kamata Saudiyya Ta Daina Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gida Na Lebanon

19:21 - January 13, 2022
Lambar Labari: 3486816
Tehran (IQNA) Kungiyar Hizbullah ta kirayi masarautar Saudiyya da ta bar kasar Lebanon ta zauna lafiya.

A yayin cika shekaru shida da shahadar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr, Sayyid Hashem Safiyuddin ya yi kira ga Saudiyya da ta kawo karshen tsoma bakin da take yi a cikin harkokin cikin gida na kasar Labanon, tare da bayyana hakan a matsayin daya daga cikin ayyukan cin fuska ga al’ummar kasar.

Sayyid Hashem Safiyuddin, shugaban majalisar zartaswa ta kungiyar Hizbullah, a wajen bikin cika shekaru shida da shahadar Sheikh Nimr al-Nimr, ya jaddada cewa wannan shahidi mai daraja bad an tawaye ba ne,  maimakon haka ma an san shi ne da kyawawan halaye da kishin kasa, kuma kisan da aka yi masa na siyasa ne zalla.

Sayyid Hashem Safi al-Din ya bayyana cewa, Sheikh Nimr ya kasance daga cikin mutane masu son a samu daidaito a tsakanin al’ummar Saudiyya da kuma masu rike da madafun iko a kasar, to amma babbar matsalar ita ce masu iko ba su son a fada musu gaskiya, kuma saboda  gaya msuu gaskiya da yake yi ne suka kashe shi.

Shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah ya kara da cewa: Muna shaida wa Amurka da Saudiyya da ‘yan korensu a Lebanon cewa; ba ku fahimci karfin wannan tsayin daka da gwagwarmaya ba, amma ku sani cewa tsayin dakan Hizbullah da sauran masu gwagwarmaya ne ya ‘yantar da kasar Lebanon, har ta iya wanzuwa a matsayin kasa mai  cin gashin kanta.

Ya ce; Muna shaida wa duniya cewa ba za mu bari wani ya kira mu da sunan ‘yan ta’adda ba,” inji shi, Ba za mu taba  yin shiru a kan haka ba.

 

 

 

4028250

 

captcha