IQNA

UAE Ta Roki Amurka Da Ta Sanya Ansarullah Ta Yemen Cikin 'Yan Ta'adda, Amurka Ta Ce Ta Nazarin Yin Hakan

16:51 - January 20, 2022
Lambar Labari: 3486844
Tehran (IQNA) bayan da UAE ta roki Amurka da ta santa Ansarullah ko Alhuthi a cikin 'yan ta'adda Biden ya ce suna yin nazari kan hakan sakamakon harin martani da suka kai kan UAE.

Biden Ya Yi Barazanar Sake Saka Ansarullah Cikin Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’addaShugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi barazanar sake mayar da sunan kungiyar Ansarullah ta Yemen da aka fi sani da Alhuthi a cikin jerin kungiyoyin da Amurka ke kira na ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Biden ya bayyana hakan ne sakamakon harin ramuwar gayya da da kungiyar ta mayar ne kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ta hanyar harba makamai masu linzami da kuma jirage marasa matukia kan tankuann maid a filayen sauka da tashin jiragen sama na Dubai da Abu Dhabi.

Biden ya ce bisa la’akari da hare-haren da kungiyar ta kai kan UAE, a halin yanzu Amurka tana yin nazarin sake mayar da kungiyar a cikin jerin kungiyoyin da take kira na ‘yan ta’adda a duniya, bayan da aka cire sunanta a shekarar da ta gabata, bayan da gwamnatin Trump ta saka kungiyar a cikin jerin kungiyoyin na ‘yan ta’adda.

A nata bangaren gwamnatin hadaddiyar daular larabawa wadda jakadanta a Amurka Yusuf Al-Utaibi shi ne ya roki gwamnatin Biden data dauki matakain saka Ansarullah cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda, ta nuna gamsuwarta da furucin na Biden.

A cikin wannan makon ne dai dakarun gwamnatin Sanaa gami da dakarun sa kai na kabilun larabawa da suke mara musu baya da suka hada da Ansarullah, suka kai hare-haren mayar da martani kan UAE, biyo bayan munan hare-haren da ita ma ta kaddamara cikin Yemen, musammana yankinan Shibwa da kuma Ma’arib, da nufin mamaye wadannan yankuna, musamman Maarib mai arzikin man fetur.

 

 

4029982

 

 

captcha