An fara gudanar da wannan taro ne a jajibirin zagayowar ranar haihuwar Sayyida Zahra (AS) kuma ana ci gaba da gudanar da shi har tsawon mako guda.
"Bikin ya hada da shirye-shirye na kur'ani da addini da na al'adu iri-iri wanda ya dauki tsawon mako guda," in ji Salim al-Jasani, mamba a majalisar gudanarwa a hubbaren Imam Ali kuma shugabar kwamitin shirya taron.
Ta kara da cewa: "Kafa da'irar Al-Qur'ani, bude dakin karatun kur'ani a tsangayar ilimin fikihu ta jami'ar Kufa, da gudanar da taron kur'ani a tsangayar ilimin 'yan mata na jami'ar Kufa da kuma gudanar da babban bikin makon Tsaftace harabar hubbaren Imam (AS) wani bangare ne na wannan biki."
Sannan kuma ta ce: Bude sabon ginin babban dakin karatu na jami'ar Al-Muthanna da ke kasar Iraki, da aikin ginin ofishin cibiyar Darul-Qur'ani ta Ahlus Sunna a yankin Diwaniyah na kasar Iraki wasu sassa ne na wannan bikin.