IQNA

Kasar Saudiyya ta hana maniyyata ‘yan kasar Siriya aikin hajji shekaru  11 a jere

19:45 - May 17, 2022
Lambar Labari: 3487307
Tehran (IQNA) shekara ta 11 a jere, Saudiyya ta hana 'yan kasar Siriya zuwa aikin Hajjin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Watan cewa, ministan kula da harkokin addini na kasar Siriya Mohammed Abdul Sattar Al-Sayed ya ce kawo yanzu kasar Saudiyya ta hana alhazan kasar ta Siriya zuwa aikin hajjin bana, kuma ta ki sanya hannu kan wata yarjejeniyar aikin hajji tsakanin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Siriya da ma'aikatar hajji da Umrah ta Saudiyya.

A wata hira da ya yi da jaridar Al-Watan ta kasar Siriya, Abdul Sattar Al-Sayed ya ce: 'Yan Saudiyya sun shafe shekaru 11 suna siyasantar da aikin Hajji, yayin da aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci kuma ba mallakin Al-Saud ba ne.

Al-Sayyid ya yi nuni da cewa kason Syria na aikin Hajji daya ne cikin dubu daya, wanda hakan ke nuna cewa sama da alhazai 20,000 ne za a ba su damar sauke farali.

A nasa bangaren, dan majalisar dokokin kasar Syria, Mohammad Khair al-Aqam, ya tabbatar da cewa, ga dukkanin alamu Saudiyya ba za ta bari ‘yan kasar Syria su yi aikin Hajji ba, ganin cewa har yanzu ba mu ga wani sauyi ba game da manufofin Saudiyya kan kasar Syria.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Watan ya ce: Saudiyya na ci gaba da siyasantar da aikin Hajji tare da haramtawa 'yan kasar Siriya aikin Hajji tun daga shekara ta 2011, a lokacin da kasashen turai da Isra’ila gami da wasu gwamnatocin larabawa suka shirya wa kasar makirci tare da haifar da yaki a  cikinta, da mara baya ga ‘yan ta’adda daga kasashen duniya domin kifar da gwamnatin kasar, amma ba su yi nasara ba.

Al-Akam ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar Saudiyya ta yi amfani da annobar Corona a matsayin uzuri don rage yawan mahajjata zuwa wurare masu tsarki: "Hajji shi ne rukunnan Musulunci na biyar, kuma wannan wani aiki ne na musulmi."

Ya kara da cewa: Kasashe da dama sun yi kira da kada a siyasantar da aikin musulmi, kuma suna son kafa wani kwamiti na hadin gwiwa na kasashen musulmi da za ta tafiyar da ayyukan musulmi na duniya musamman aikin hajji da Umrah, maimakon lamarin ya ci gaba da zama  karkashin ikon wasu ‘yan tsiraru bisa manufofin siyasarsu, Domin wadannan wurare masu tsarki na dukkan musulmi ne.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4057772

captcha