IQNA

Majalisar dokokin Iraki ta zartar da wata doka da ta haramta kulla alaka da Isra'ila

14:24 - May 26, 2022
Lambar Labari: 3487345
Tehran (IQNA) 'Yan majalisar dokokin kasar Iraki baki daya sun amince da daftarin dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cewar daftarin kudurin, daga cikin muhimman abubuwan da wannan doka ta kunsa,  duk wani aiki na siyasa, tsaro, tattalin arziki, fasaha, al'adu, wasanni da kimiyya tare da gwamnatin sahyoniyawa ba halastacce ba ne.

Wakilan kasar Irakin sun kuma rera taken nuna adawa da duk wani yunkuri daga kowane bangare ne na 'yan sisa da ke neman daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahyoniya."

An gabatar da kudirin a gaban majalisar bisa shawarar bangaren Sadr tare da goyon bayan duk wani yunkuri na siyasa na Shi'a (Coordination Framework Coalition) tare da zartas da shi da kuri'u mafi rinjaye, don haka ya rufe kofa ga masu neman kulla alaka ta boye da gwamnatin Isra’ila.

Jagoran kungiyar Sadr Sayyid Muqtada al-Sadr ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka kada kuri'ar amincewa da kudurin tare da yin kira ga al'ummar Iraki da su gudanar da addu'o'in godiyar raka'a biyu tare da fitowa kan tituna domin nuna farin cikinsu.

Dokar ta kunshi muhimman batutuwa guda 10, wadanda manufarsu ita ce kare kimar kasa, Musulunci da mutuntaka na kasar Iraki da kuma manufofin al'ummar Iraki wajen kare al'ummar Palastinu da hana duk wani yunkuri na daidaitawa ko kulla alaka da Isra’ila.

Abin tuni  nan shi ne cewa, a baya dokar hukunta manyan laifuka ta kasar Iraki ta haramta duk wani yunkuri na kulla alaka da wannan gwamnati ta yahudawa mai cin zarafin bil adama.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4059866

captcha