IQNA

Darajar tunani a Musulunci

15:22 - May 28, 2022
Lambar Labari: 3487351
Tehran (IQNA) Kira zuwa ga yin tunani yana daya daga cikin manya-manyan nasihohi a Musulunci kuma yana da kima da muhimmanci har Manzon Musulunci (SAW) ya ce: "Sa'a guda ta tunani ta fi daraja fiye da ibadar shekaru 60 ba tare da tunani ba".

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Sa’ar tadabburi ta fi daraja fiye da ibadar shekara 60 ba tare da tadabburi ba”. An nakalto wannan hadisi a cikin littafin “Al-Risalah fi al-Ahadith al-Nabawiyyah” na Hussein bn Ali Wa’iz Kashfi (masanin falaki kuma mai tafsirin Alkur’ani mai girma, an haife shi a Sabzevar, Iran, 1436-1504).

Allamah Majlisi yana cewa dangane da haka:

Wasu dattijai suna cewa tunani ya fi girma domin zuciya ita ce aiki (hankali) kuma zuciya ita ce a gaba mafi girma kuma aikinta ya fi sauran gabobi. “Lokacin da Allah Ya ce, ‘Ka tsayar da sallah domin ambatona, sai ya sanya sallah ta zama hanyar tunawa da zuciya.

A mahangar Musulunci, ba kowane tunani ba ne ibada, sai dai tunanin ibada da ke kan tafarkin juyin halittar dan Adam da hikimomin ubangiji dake tatatre da halitta da kuma manufar hakan. A cikin Alkur'ani mai girma mas'alar tunani an yi bayani dalla-dalla, tunani a kan komai yana da nasa sakamakon, kuma za mu ambaci wasu misalansa a kasa:

Yin tunani a cikin halitta shi ne sakamako imani daga hakikanin sanin Allah da manufarsa ta yin halitta (Al-Imran, 191).

Yin la’akari da tarihin wasu shi ne sakamakon nasiha da daukar darasi (Araf, 176).

Yin tunani game da ƙazantar duniya da abubuwan da suke bayyanawa, shine sakamakon son zuciya, da kuma sakamakon yin taƙawa. (Nisa'i, aya ta 77)

Yin tunani game da ni'imomin Allah shine sakamakon da ke kaiwa ga  godiyar Allah. (Ibrahim, aya ta 7)

Yin tunani a kan taimakon Allah da kuma ikonsa na yin hakan, shi ne ke sanya fata a cikin rayuwa da kaunar samun falala daga gare shi (Romawa, 47)

Mohammad Baqir bin Mohammad Taqi Majlisi (1628-1699 miladiyya) wanda aka fi sani da Allamah Majlisi ya kasance daya daga cikin mashahuran maruwaita da malaman fikihu na Shi'a da suka rayu a birnin Isfahan na kasar Iran. Shahararren aikinsa shi ne Baharalanvar, wanda ya tattaro hadisan Annabi da ma’asumai a cikin mujalladi 110.

 

 

captcha