Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sawa Al-Akhbariya cewa, hukumar kula da wuraren ibada guda biyu a kasar Saudiyya ta shirya wani baje koli domin fadakar da mahajjata sana’ar saka labulen Ka’aba a haramin Makkah.
A cikin wannan baje kolin, mahajjata sun koyi fasahar saka labule na Ka'aba, da zane-zane da hanyoyin saka kalmomi da ma'anonin sa, tare da gudanar da wani takaitaccen bangare na wannan fasaha a karon farko.