IQNA

Shirye-shiryen a hubbaren Imam Ali na makokin Tasu’a da Ashura

15:14 - August 05, 2022
Lambar Labari: 3487642
Tehran (IQNA) A jajibirin Tasu'a da Ashura na Hosseini, hubbaren Imam Ali (AS) ya dauki matakan saukaka zaman makoki na mahajjata da tawagogin masu ziyara a hubbaren .

Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Tare da haɗin gwiwa tsakanin hubbaren Imam Ali da tawagogin Hosseini , an shirya shirye-shiryen sauƙaƙe shigar ƙungiyoyin makoki daga titunan da ke kewaye zuwa wurin ibada na Alavi.

Masu hidimar tsattsarkan wuraren ibada  suna ƙoƙarin samar da mafi kyawun wuri don taron  makoki.

Har ila yau, a ci gaba da gudanar da ayyukan fage da bayar da hidima ga jerin gwanon tawagogin masu ziyara a cikin kwanaki goma na farko na watan Muharram, ma'aikatan fasaha da injiniya na hubbaren Imam Ali sun yi yashi mai fadin murabba'in mita 3500 kusa da farfajiyar Imam Husaini (a.s.) don gudanar da ayyukan raya taron makokin.

Tun da farko dai a jajibirin watan Muharram an kafa rubutun Tarmah mai dauke da wani bangare na baitocin wakar Sayyid Haider Hilli  kan batun Ashura a hubbaren Amirul Muminin (AS).

 

 

4075887

 

captcha