Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Furat News ya bayar da rahoton cewa, Fazel Oz, ma'aikacin da ke kula da tsare tsare na hubbaren Imam Husaini (AS) ya sanar da cewa: maziyarta da dama daga kasashen duniya daban-daban ne suka shiga kasar Iraki domin halartar taron tasu'a da tarukan Ashura na bana.
Ya kara da cewa: Tun a ranar farko ta watan Muharram birnin Karbala ya samu halartar maziyarta Imam Husaini masu dimbin yawa, kuma wannan adadin ya kasance ba a taba ganin irinsa ba tun shekara ta 2003.
Fazel Oz ya fayyace cewa: Baya ga 'yan kasar Iraki da suka shigo Karbala daga larduna daban-daban na wannan kasa, masun ziyara da dama daga kasashen duniya daban-daban sun yi tattaki zuwa Karbala domin halartar zaman makokin Tasu'a da Ashura Husaini a kusa da haramin Imam Husaini da Abbas (amincin Allah ya tabbata a gare su)
Ya kara da cewa: A shekarun baya an takaita adadin maziyarta ne a daren 10 ga watan Al-Muharram, amma a bana mun ga dimbin maziyarata mutane tun daga ranar farko ga watan Al-Muharram.