A rahoton da shafin Arabi 21 ya bayar,
An zargi Kerr Starmer, shugaban jam'iyyar adawa ta Labour a Ingila, da hada baki da wasu domin kara matsin lamba a kan Apsana Begum, wata musulma 'yar majalisar dokoki, bayan da ta yi korafi kan cin zarafin da mata suke fuskanta a rayuwa ta zamantakewar iyalai a kasar.
Shafin yada labarai na Nuwara ya ruwaito wani kwararre kan lamurra da suka shafi matsalolin zamantakewar iyalai yana bayyana cewa: Bayan Begum ta kira kanta a matsayin wadda ta tsira daga irin wannan matsala, jam'iyyar Labour ta nemi daukar matakan hana Begum tsayawa takara a zabe mai zuwa.
Begum, mai shekaru 32, ta lashe kujerarta a yankin Poplar & Limehouse a shekarar 2019 kuma ta zama 'yar majalisar dokoki mace musulma mai sanye da lullubi ta farko da ta shiga majalisar dokokin Burtaniya.
John McDonnell, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar kuma tsohon ministan kudi a gwamnatin Burtaniya, ya bayyana goyon bayansa ga Begum, sannan kuma ya aike da wata wasika zuwa ga Starmer, inda ya bukace shi da ya dakatar da yunkurinsa na cire Begum daga shiga zabuka masu zuwa.