IQNA

Burtaniya Na Shirin Dauke Ofishin Jakadancinta Da Ke Isra'ila Daga Tel Aviv Zuwa Quds

15:26 - September 22, 2022
Lambar Labari: 3487894
Tehran (IQNA) Firaministan Birtaniya Liz Truss ta shaidawa takwaranta na Isra'ila Yair Lapid cewa tana nazarin matakin mayar da ofishin jakadancin kasarta daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

Wata mai magana da yawun gwamnatin Burtaniya ta ce Truss ta sanar da Lapid yadda ta yi nazari kan inda ya kamata ofishin jakadancin Birtaniya a Isra'ila ya kamata ya kasance a halin yanzu, ta sheda hakan ne yayin ganawar da suka yi a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Wani mai magana da yawun Lapid ya tabbatar wa jaridar "Times of Israel" wannan al'amari.

A watan da ya gabata, kafin ta zama Firayim Minista, Truss ta ce za ta yi nazari kan matakin da Birtaniya ta dauka na ci gaba da rike ofishin jakadancinta a Tel Aviv idan ta zama firayim minista, inda take tunanin cewa za ta mayar da shi zuwa birnin Quds.

Sanarwar da aka fitar a watan Agusta ta sha suka daga tsoffin jami'an diflomasiyyar Burtaniya, 10 daga cikinsu sun rubuta wa jaridar The Times cewa, matakin mayar da ofishin jakadancin Burtaniya zuwa ya kamata ya kasance ne bayan kafa kasar Falasdinu.

A shekarar 2018 gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus, kamar yadda Honduras, Guatemala da Kosovo suka yi, wanda Burtaniya karkashin Truss ke shirin bin sahun Amurka a wurin daukar irin wannan mataki.

4087251

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Burtaniya kudus ofishin jakadanci karkashin
captcha