IQNA

Makarancin Kur’ani Daga Masar yana karanta ayoyi daga suratu maryam

Tehran (IQNA) – Yau ce ranar kirsimati da ke bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa Almasihu (AS)

A wannan karon an fitar da faifan bidiyo da ke dauke da karatun kur'ani mai tsarki na wani dan kasar Masar Abdul Fattah al-Taruti a shafukan sada zumunta.

A cikin wannan faifan, Taruti ya karanta aya ta 15 da 16 a cikin suratul Maryam: “Aminci ya tabbata a gare shi, a ranar da aka haife shi da ranar da zai mutu, da ranar da ake tayar da shi yana mai rai. Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, yadda ta yi hijira daga mutãnenta zuwa wani wuri daga gabas, kuma ta riƙi wani shãmaki, baicinsu."