IQNA

An Kawata Haramin Sayyiduna Abbas gabanin bukukuwan Sha'aban

Tehran (IQNA) – An kawata hubbaren  Sayyiduna Abbas (AS) da ke Karbala a kasar Iraki da furanni gabanin zagayowar ranar bikin Sha’aban.

Ranar 3, 4 da 5 ga watan Sha’aban (24, 25, da 26 ga watan Fabrairun wannan shekara) ne ake gudanar da maulidin Imam Husaini (AS) da Sayyid Abbas (AS) da Imam Sajjad (AS) bi da bi.