IQNA

An kawata Masallacin Jamkaran Gabanin Maulidin Imam Zaman

Tehran (IQNA) – An kawata Masallacin Jamkaran da ke kusa da birnin Qom na kasar Iran da fitilu da tutoci a daidai lokacin da Maulidin Imam Zaman (AJ)  ke gabatowa.

Ranar 15 ga watan Sha’aban, ko kuma Nisfu Sha’aban, wadda ke cika maulidin Imam Zaman (AS), ta zo ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris na wannan shekara.

A kowace shekara miliyoyin mabiya mazhabar shi'a a duniya suna gudanar da bukukuwan girmama  wannan rana.

A wannan gagarumin biki, masallacin Jamkaran yana samu halartar dubban daruruwan maziyarta.