IQNA

Yunkurin wani Ayyukan Fasaha dan Pakistan na kammala kur'ani mafi girma a duniya

Tehran (IQNA) Mai fasahar rubutu dan  Pakistan Shahid Rassam yana kamala aikin  rubutun kur'ani mafi girma a duniya tare da tawagarsa mai mutane 200 a birnin Karachi na Pakistan.

Ana yin wannan aikin ne a kan zane-zane na aluminum mai lullubin zinare, wanda ya bambanta da nau'ikan Alqur'ani da aka saba da su, waɗanda galibi ana rubuta su akan takarda, ko fata. An baje kolin wani bangare na wannan Al-Qur'ani a wajen baje kolin Dubai na shekarar 2020.