IQNA

Wata kungiyar agaji ta Saudiyya na Rarraba abinci miliyan 1.2 a cikin watan Ramadan

14:34 - March 26, 2023
Lambar Labari: 3488865
Tehran (IQNA) Wata kungiyar agaji a kasar Saudiyya tana raba abinci kimanin miliyan daya da dubu dari biyu a cikin watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News cewa, kungiyar bayar da kyauta ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa ta fara raba buda baki da kuma sahur ga maniyyata a cikin watan Ramadan mai alfarma.

A bana, kungiyar agajin na shirin raba abinci akalla miliyan 1.2.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya bayar da rahoton cewa, za a gudanar da gagarumin rabon kayan abinci ne ga masallata a masallacin Harami da ke Makkah da kuma masallacin Annabi da ke birnin Madina.

Kungiyar ta kuma sanar da cewa masu aikin sa kai 750 ne za su yi hidimar alhazai a cikin wannan wata mai alfarma.

A ranar Alhamis aka shiga watan Ramadan a kasar Saudiyya.

 

 

 

4129851

 

captcha