IQNA

Bukin Norouz Da Azumin Ramadan A Hasumiyar Milad

Tehran (IQNA) - Hasumiyar Milad da ke birnin Tehran na gudanar da bikin Nowruz da na Ramadan har zuwa karshen wata mai albarka.

Bikin Nowruz da Ramadan na hasumiyar Milad  ya fara ne daga farkon shekara ta 1402 hijira shamsiyya a dandalin yawon shakatawa  na Milad Tower tare da shirye-shiryen farin ciki na Nowruz, kuma har zuwa karshen watan Ramadan, wannan rukunin zai dauki bakuncin masu yawon bude ido daga rana har zuwa dare.