IQNA

An Gudanar da Taro na Ƙasa da Ƙasa kan Tsoffin Rubuce-rubucen Alkur'ani a Indonesia

IQNA – An gudanar da wani taro na ƙasa da ƙasa mai taken “Tsoffin Rubuce-rubucen Alkur'ani da Matsayinsu a Tarihin Alkur'ani Mai Girma: Darussa daga Rubutun Mashhad (Codex Mashhad)” a birnin Jakarta, babban birnin ƙasar Indonesia. Taro ya samu halartar kusan farfesoshi da masu bincike 200 a fannin nazarin Alkur'ani, ciki har da tawaga daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.