IQNA

Musulmi Da Kiristoci Sun Yi Gargadi Kan Ayyukan Yahudawa A Qods

20:15 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963521
Bangaren kasa da kasa; Majalisar hadin gwiwa tsakanin musulmi da kiristoci ta gargadi dangane da irin take-taken yahudawan sahyuniya na tsokana a birnin Qods da kuma masallacin aksa mai alfarma.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da kamfanin dillancin labaran saba ya bayar a shafinsa na yanar gizo an bayyana cewa, Majalisar hadin gwiwa tsakanin musulmi da kiristoci ta gargadi dangane da irin take-taken yahudawan sahyuniya na tsokana a birnin Qods da kuma masallacin aksa mai alfarma da kewaye.

Bayanin ya kara da cewa majalisar ta yi wannan gargadin bisa la'akari da cewa yahudawan sahyuniya na daukar wasu matakai na mayar da dukkanin wurare masu alfarma a birnin mallakin yahudawa.

621953





captcha