IQNA

An Bukaci Mahukuntan Bahrain Da Su Saki Seikh Ali Salman

13:34 - January 30, 2019
Lambar Labari: 3483338
Bangaren kasa da kasa, a shekarar da ta gabata ce dai wata kotun kasar ta masarautar Bahrain ta yanke hukuncin zaman kurkuku ga sheikh Ali Salam na daurin shekaru tara, amma daga bisani kuma kotun ta sake tayar da hukuncin bisa hujjar cewa akwai wasu tuhumce-tuhumce da zata kara.

Kafanin dillancin labaran iqna, ranar Litinin ne aka sake gabatar da mutanen uku a gaban kotun daukaka kara, a watan Febrairu na dubu biyu da sha daya ne al'ummar kasar Bahrain suna fara yunurin neman kawo sauyi a fagen siyasar kasar da kuma neman 'yanci ga al'ummar kasar mai bin tsarin mulukiya.

Masarutar kasar ta murkushe yunkurin al'ummar kasar ta hanyar amfani da karfi da kuma jefa shugabannin 'yan hamayya cikin kurkuku.

Kungiyar Kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta Bahren ta yankewa shugaban jam'iyar Alwufaq shekh Ali Salman zalinci ne

Samah Hadid babban daraktan kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa Amnesty International bangaren gabas ta tsakiya na cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta kasar Bahren ta yankewa shugaban Jam'iyar Alwufaq  Zalinci ne.

Kungiyar ta bayyana hukuncin a matsayin katsa landan na mahukuntar masarautar Ali khalifa a harakokin shari'ar kasar

Har ila yau, Kungiyar ta bukaci gwamnatin kasar Bahren da ta gaggauta sakin Shekh Ali Salman ba tare da wani sharadi ba.

A jiya Litinin ne kotun daukaka karan kasar Bahren ta tabbatar da daurin rai da rai da wata kotun kasar ta yankewa Shekh Ali Salman shugaban jam'iyar musulinci ta Alwufaq da shekh Hasan Sultan gami da Ali Aswad tsofofin 'yan majalisar dokokin kasar da ake tsare da su tun a ranar ashirin da hudu ga watan 24 ga watan Oktoban shekarar 2018 din da ta gabata bisa zargin cewa sun yi wa gwamnatin kasar qatar leken asiri.

A matsayin mayar da martani jam'iyar Alwufaq ta sanar da cewa za ta ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da zalinci masarautar Ali Khalifa a kasar.

3785428

 

 

 

 

captcha