IQNA

Taro A Uganda Kan Cika Shekaru 40 Da Samun Nasarar Juyin Islama A Iran

17:30 - February 04, 2019
Lambar Labari: 3483345
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taron a birnin kampala na kasar Uganda kan zagayowar lokacin cikar shekaru arba’in da samun nasarar juyin juya halin Iran.

Kafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da zaman taron a birnin kampala na kasar Uganda kan zagayowar lokacin cikar shekaru arba’in da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a wajen taron an samu halartar malaman addini da kuma masana gami da malaman jami’oi. Inda aka gabatar da laccoci kan wannan juyi da kuma tasirinsa a cikin kasasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya musamman masu tasowa.

Wannan taro ya mayar da hankali kan irin muhimman darussan da juyin juya halin Iran yake koyarwa ga sauran al’ummomin duniya, musamman mas neman samun ‘yanci daga mulkin mallakar kasashe masu girman kai  a wanann zamani.

Daga cikin bayanan da aka gabatar a kwai wadanda suka tabo yadda juyin juya halin ya fadakar da a’ummomi kan mikewa su dofara da kansu, maimakon dogaro da turawa a kowane lokaci.

Kasar Iran ta samu gagarumin ci gaba ta fuiskoki daban-daban sakamakon dogaro da kanta a cikin tsawon shekaru arba’in na juyin juya halin muslunci.

Daga karshe an baje kolin wasu daga cikin hotunan juyin juya haling a mahalrta domin ganin wasu daga cikin abubuwan da suka faru.

3787175

 

captcha